Wani tauraron dan adam mai suna Starship SN11 da kamfanin SpaceX mallakar dan kasuwar Amurka Elon Musk ya harba zuwa duniyar sama ya yi bindiga a lokacin da ake gwajin sa a karo na 4.
A lokacin da ake gwajin a kamfanin SpaceX da ke garin Cameron na jihar Texas din Amurka, tauraron SN11 da aka harba cikin nasara zuwa sama, ya yi bindiga a lokacin da ya ke kokarin sauka.
Jim kadan bayan jami'an kamfanin sun bayar da bayanai game da fashewar, sai aka dakatar da nuna aiyukan gwajin kai tsaye.
News Source: ()