Wadanda aka yi wa allurar riga-kafin Corona ne kadai za su shiga manyan kantina a Saudiyya

Wadanda aka yi wa allurar riga-kafin Corona ne kadai za su shiga manyan kantina a Saudiyya

A Saudiyya an bayyana cewa, daga watan Agusta duk wadanda ba a yi wa allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19) ba, to ba za su shiga manyan kantinan saye da sayarwa ba.

Labaran da tashar talabijin ta kasa ta fitar na cewa, sakamakon daukar matakin da Ma'aikatar Kasuwanci ta yi, daga ranar 1 ga Agustan 2021 babu wanda zai shiga manyan kantinan saye da sayarwa sai wanda aka yi wa allurar riga-kafin Corona a kalla sau 1.

Ya zuwa yanzu an yi amfani da allurar riga-kafin Corona miliyan 15,7 a Saudiyya.

 


News Source:   ()