
Turkiyya za ta bayar da taimakon kayan kula da lafiya masu yawan tan 12 ga Sanagal.
Shugaban Kasar Sanagal Macky Sall ya fitar da sanarwa ta Twitter game da tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
A sakon da ya fitar, Sall ya shaidawa Erdogan cewa, suna tare da jama'ar Turkiyya a wannan lokaci da annobar gobarar daji ta addabe su.
Shugaban na Sanagal ya kuma ce, a tattaunawar tasa da Erdogan an amince kan Turkiyya za ta aikawa Sanagal da taimakon kayan kula da lafiya masu yawan tan 12 don yaki da annobar Corona.
News Source: ()