Turkiyya ta sake bayar da taimakon alluran riga-kafin Corona kwaya dubu 40 ta kamfanin Sinovac ga Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus.
Ya zuwa yanzu Turkiyya ta aikawa da Cyprus allurai guda dubu 140.
Sanarwar da Firaministan Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus Ersan Saner ya fitar ta ce,
"Tare da al'umarmu da taimakon Turkiyya, muna ci gaba da yaki da annobar Corona. A daren Litinin din nan Turkiyya ta sake aiko mana da taimakon allurai dubu 40 na Sinovac muna mika godiyarmu ga asalin kasarmu ta Turkiyya. Mu daure mu yi aiki da dokokin hana fita."
News Source: ()