Turkiyya ta sake aika taimakon alluran riga-kafin Corona zuwa Arewacin Cyprus

Turkiyya ta sake aika taimakon alluran riga-kafin Corona zuwa Arewacin Cyprus

A karkashin aiyukan yaki da annobar Corona (Covid-19), Turkiyya ta sake aikawa da allurai dubu 50 na kamfanin Sinovac na China zuwa Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus.

Jirgin saman Ma'aikatar Lafiya ta Turkiyya dauke da alluran ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Ercan a daren Larabar nan.

An mika alluran ga jami'an Ma'aikatar Lafiya ta Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus.

Ya zuwa yanzu Turkiyya ta aika da taimakon alluran riga-kafin Corona dubu 190 zuwa Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus.


News Source:   ()