Ministan makamashi da albarkatun kasar Turkiyya Fatih Donmez ya ja hankali game da mahimmancin hadin kai da kasashen Afirka inda ya ce, darajar hannun jarin da Turkiyya ta zuba a Afirka ya kai dala biliyan 6.
Donmez ya bayyana cewa, ya yi imanin Turkiyya da Angola za su iya aiwatar da muhimmiyar hadin gwiwa a bangaren makamashi inda ya kara da cewa,
"Darajar kasuwar hannun jarin da Turkiyya ta zuba a Afirka ya kai dala biliyan 6. Adadin ayyukan da 'yan kwangilar Turkiyya suka yi a fadin nahiyar ya wuce kwara 1500, kuma kiman tattalin arzikin ayyukan ya wuce dala biliyan 70."
Donmez ya ce a taron karo na 2 na Kwamitin Hadin Kan Tattalin Arzikin Turkiyya da Angola (KEK), wanda ya halarta ta taron bidiyo konferance, ya ce Turkiyya na yin aiki ne bisa hanyar samun nasara a duk kasar da ta yi hadaka da ita.
Donmez ya bayyana cewa, a cikin wannan watan za a sanya hannu kan Yarjejeniyar Sufurin Jiragen saman, wanda zai ba wa kanfanin jiragen saman Turkiyya naTurkish Airlines damar shirya jigilar fasinja da jigilar kaya zuwa Angola.
Diamantino Pedro Azevedo, Ministan Man Fetur da Albarkatun Kasar Angola, ya bayyana cewa , na yi imanin kasashen biyu za su ba da gudummawa ga hadin gwiwa a fannin makamashi a lokuttan dake tafe.