Turkiyya ta aike da sakon jaje da ta'aziyya ga Venezuela sakamakon samun rayuka da ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa suka janyo a kasar.
Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta shaida cewa, sun yi bakin ciki da samun labarin afkuwar ambaliya da zaftarewar kasa a Merida da ke yammacin Venezuela inda mutane da dama suka mutu.
Sanarwar ta ce, "Muna mika ta'aziyya da gwamnati, kafatanin al'uma da makusanta wadanda suka mutu sakamakon ibtila'in ambaliyar ruwa, muna fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata."
News Source: ()