Turkiyya ta gano sabbin rijiyoyin man fetur

Turkiyya ta gano sabbin rijiyoyin man fetur

Shugaba kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa bayan gano gas mai yawan cubic mita biliyan 405 a cikin tekun Bahar Maliya, sun fara samun labari masu dadin ji a binciken ma'adanai da ake yi a yankunan kasar. 

Shugaba Erdogan ya kara da cewa,

"Mun gano sabbin rijiyoyin mai 3 a  cikin wata 1 da ya gabata," 

Shugaban Wanda shi ne kuma Shugaban Jam'iyyar Adalci da Cigaba (AK Party) ya yi jawabi a Wajen Tattaunawar Shugabannin  Jam’iyyun Demokradiyya.

Da ya ke  jaddada cewa yana fatan karin bunkasar  tattalin arziki kamar yadda aka samu a wannan shekarar, ya kara da cewa,

“Bayan da muka gano gas na cubic mita biliyan 405 a cikin Bahar Maliya, mun fara samun sakamakon aikinmu a yankunan kasa. Mun gano mai a cikin sabbin rijiyoyi 3 a cikin wata 1 da ya gabata. " 

Erdogan ya kara da cewa, 

"Matsakaicin yawan mai da ake samarwa a cikin gida a shekarar 2021 ya wuce ganga dubu 61 bayan gano sabbin rijiyoyin uku"

 

Da ya tabo batun aiki kan sabon kundin tsarin mulki, Shugaba Erdogan ya tunatar da cewa,

"Zai yi kyau sosai idan har za mu iya karbar sabon kundin tsarin mulki a Majalisar Dokokin Turkiyya (TBMM) tare da cimma matsaya daya kuma mu gabatar da shi ga yadda al'ummarmu za su faidantu. Manufarmu ita ce samar da ingantaccen yanayi ga kowa"

 


News Source:   ()