Kasar Turkiyya ta fitar da ruwan zuma a cikin watannin biyun farkon shekarar bana zuwa kasashe 27 har na dala miliyan 4.1.
Kamar yadda Kungiyar Fitar da Kayayyaki na Yankin Gabashin Bahar Rum ta sanar a watannin Janairu da Febrairu zuwa kasashe 27 Turkiyya ta fitar da ruwan zuma na ton 1039 wanda ya kama na kudi dala miliyan 4 da dubu 143 da 597.
Kasar da aka fi fitar da ruwan zuman ita ce Jamus da na miliyan 1 da dubu 304 da 114, sai Amurka da na miliyan 1 da dubu 148 da 989 sai Kuwait da na dubu 215 da 537.
An fitar da adadin ruwan zuma na dala dubu 316 da 277 daga Bahar Maliya ta Gabas a watan Janairu zuwa Fabrairu zuwa kasashen Jamus, Ingila, Bahrain, Pakistan, Jamhuriyar Jama'ar Sin, Qatar, Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ruwan zumar da ake fitarwa daga yankin ya karu da kashi 74 cikin dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, wanda aka samu dala 181 dubu 891.