Kayayyakin da Turkiyya ke fitarwa ya karu da kaso 109.2 a cikin dari inda ya kai na zunzurutun kudi har dala biliyan 18 da miliyan 786 cikin watan Afrilu idan aka kwatanta da na wannan watan na shekarar da ta gabata.
An sanar da bayanan cinikayyar kasashen waje na wucin gadi a watan Afrilu, wanda aka kididdige tare da hadin gwiwar Cibiyar Tattalin Arziki ta Turkiyya (TUIK) da kuma Ma'aikatar Kasuwanci.
A kan haka, fitar da kaya ya karu da kaso 109.2 a cikin watan Afrilu idan aka kwatanta da na watan da ya gabata inda ya kai dala biliyan 18 da miliyan 786.
Fitar da kaya zuwa kasashen waje ya karu da kaso 33.1 a cikin watannin Janairu zuwa Afrilu idan aka kwatanta shi da na shekarar da ta gabata kuma ya kai dala biliyan 68 da 739.