
Shekaru dubu 4 kenan da ake da kwaranda a duniya, amma ba a san yaushe ne aka fara samun ma’adanin kasar a Turkiyya ba, amma ana ganin an fara sarrafa shi shekarun 1800. Ma’adanin kwaranda sama da 400 da ake amfani da su a bangrori daban-daban, na daya daga cikin ma’adanan kasa mafiya muhimmanci a Turkiyya. Ana amfani da shia bangaren masana’antun tsaro zuwa yin gilasai, yin seramic, bangaren noma da tsafta. Ana samar da wani bangare na kayan da ake samar da nukiliya da su da wannan ma’adani na kwaranda. Shi ya sa ake kiran kwaranda da sunan ma’adani na nan gaba. Ba za a iya kayyade amfanin kwaranda ba. Ana amfani da shi a masana’antu da dama, kuma yadda ya ke ba ya cutar da muhalli na kara ba shi kwarjini.
A Turkiyya akwai ma’adanin kwaranda da zai ishi duniya har nan da shekaru 400 zuwa 500, wanda hakan ke bakantawa Amurka da Rasha. Wannan arziki ne da babu irin sa a wata kasa in banda Turkiyya.