
Ayarin kayan taimako na Kungiyar Bayar da Agaji ta Turkiyya ta 'Red Crescent' sun isa Zirin Gaza inda suka wuce ta kofar kan iyaka ta Refah.
Kayan taimakon a cikin motocin tirela 10 sun bi ta kofar Refah da ke iyakar Masar da Falasdin inda suka isa ga kungiyar 'Red Crescent' a Zirin Gaza.
A cikin kayan taimakon akwai kunshin kayayyakin abinci, magunguna, kayan tsafta da tufafi.
Tun shekarar 2006 Isra'ila ta yi wa Zirin Gaza mai mutane miliyan 2 kawanya ta kasa, sama da ruwa.
News Source: ()