Pakistan da wani kamfanin Turkiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar dala miliyan 33,46 don samar da jiragen ruwa.
Sanarwar da Ma'aikatar Sufurin Teku ta Pakistan ta fitar ta ce, a yayin taron sanya hannun a Islamabad, an samu halartyar Ministan Sufurin Teku na Pakistan Said Ali Kaydar Zaidi, Jakadan Turkiyya a Islamabad Ihsan Mustafa Yurdakul da jami'an kamfanin teku na Sanmar da ke Turkiyya.
Sanarwar ta ce, wannan yarjejeniya na da muhimmanci kwarai da gaske wajen matakan habaka alakar kasashen 2 'yan uwan juna.
A karkashin yarjejeniyar, kamfanin Sanmar na Turkiyya zai kafa reshe a Pakistan inda zai samar da jiragen ruwa na ASD guda 4 da wasu samfurin pilot guda 2.