Shugaban Kasar Aljeriya Abdulmajid Tebbun ya bayyana cewa, kasarsa da Turkiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da safarar kayayyaki a teku.
Jaridar Kasa ta Tukiyya a ranar Alhamis din nan ta buga yarjejeniyar da Shugaban na Aljeriya ya sanya hannu a kai a ranar 5 ga Mayu, kuma ta kunshi samar da jiragen ruwa, gyara su da gina tashoshin jiragen ruwa.
Tun ranar 25 ga watan Mayun 1998 aka kulla yarjejeniyar amma bangaren Aljeriya bai sanya hannu a kai ba sai yanzu. Yarjejeniyar za ta kara yawan safarar jiragen ruwa da gudanar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.
Tebbun ya kuma ce, jarin kasuwanci tsakanin Turkiyya da Aljeriya na tsakanin dala biliyan 3,5 da 4,2, kuma suna da manufar kara shi zuwa dala biliyan 5.
A wata tattaunawa da Tebbun ya yi da mujallar mako-mako ta Le Point da ke Faransa ya bayyana cewa, 'yan kasuwar Turkiyya sun zuba jarin dala biliyan 5 a kasarsa ba tare da neman wata bukata ta siyasa ba, kuma suna da kyakkyawar dangantaka da Turkawa.