Turkish Airlines ya sake cirar tuta a nahiyar Turai

Turkish Airlines ya sake cirar tuta a nahiyar Turai

Kamfanin jiragen saman Turkiyya na Turkish Airlines ya sake jirar tuta a nahiyar Turai da safarar jirage 448 a kowacce rana.

Hukumar Kula da Ingancin Safarar Jiragen Sama ta Turai (EUROCONTROL) ta bayyana alkaluman kaiwa da komowar jiragen sama a nahiyar a ranar 11 ga Mayu, inda Turkish Airlines ya zama na farko da tashi da saukar jirage 448.

Air France ne ke bin Turkish Airlines da safara 371. Wideroe ne na 3 da safara 350, Lufthansa kuma na 4 da safara 310, sai DHL Express dake na 5 da jirage 295.


News Source:   ()