Turkish Airlines na kara yawan garuruwan da yake zuwa

Turkish Airlines na kara yawan garuruwan da yake zuwa

Kamfanin jiragen sama na Turkiyya (Turkish Ailines) ya gudanar da safara ta farko zuwa garin Vancouver na kasar Kanada.

Bayan garuruwan Toronto da Motreal, Turkish Airlines ya fara tashi da sauka a gari na 3 a Kanada inda ya sauka da jirgi mai lamba TK075 a garin Vancouver.

Jirgin dauke da fasinjoji 167 ya sauka a Vancouver da misalin karfe 16.17 agogon Kanada kuma karamin jakadan Turkiyya a Vancouver Mehmet Taylan Tokmak da daraktan Turkish Airlines a Toronto Zafer Bolukbasi ne suka tarbe shi.

Turkish Airline ya kara yawan safararsa zuwa 15 a Vancouver da Arewacin Amurka inda a yanzu haka yake zuwa garuruwa 319 a duniya.

 


News Source:   ()