Kamfanin Jiragen Saman Turkiyya (Turkish Airlines) na ci gaba da yin zarra a Turai inda a tsakanin 3 da 14 ga Maris ya yi tashi sau 649 a kowacce rana.
Hukumar Kula da Ingancin Safarar Jiragen Sama ta Turai (EUROCONTROL) ta fitar da rahoton safarar jiragen sama a nahiyar a tsakanin 3 da 14 ga Maris inda Turkish Airlines ya tashi sau 649 a kowacce rana.
Kamfaninnna Turkiyyane a kan gaba inda Air France ya ke biye masa bayya da tashi sau 358.
Na 3 a jerin sunayen shi ne KLM da tashi 243, Lufthansa na 4 da tashi 231, SAS na 5 da tashi 165 sai British Airways na 6 da tashin jirage 105.