Turkish Airlines na ci gaba da yin zarra a nahiyar Turai

Turkish Airlines na ci gaba da yin zarra a nahiyar Turai

Kamfanin jiragen saman Turkiyya ya sake jan ragama a tsakanin jiragen saman nahiyar Turai da safara 518 a kowacce rana.

Hukumar Kula da Ingancin Safarar Jiragen Sama ta Turai (EUROCONTROL) ta sanar da cewa, a tsakanin 10 da 16 ga Mayu, Turkish Ailines ya tashi da sauka sau 518 a matsakaici inda ya zama a kan gaba.

Air France ne ke biyewa Turkish Ailines baya da safara 403, sai Lufthansa da safara 378 inda Rynair yake a mataki na 4 da safara 367. KLM na 5 da safara 300 inda Wideroe ya zo na 6 da safara 261.

 


News Source:   ()