Kamfanin jiragen sama na Turkiyya (Turkish Ailines) na ci gaba da zarce sa'a a nahiyar Turai inda ya yi tashi sau 797 a kowacce rana a mako dayan da ya gabata.
Hukumar Kula da Ingancin Safarar Jiragen Sama ta Turai (EUROCONTROL) ta fitar da rahoton zirga-zirgar jiragen sama a nahiyar a tsakanin 29 ga Maris da 4 ga Afrilun 2021 inda Turkish Airlines ya ke da matsakaicin tashi sau 797 a kowacce rana.
Air Lufthansa ne na 2 a jerin kamfanunnukan tashi da sauka sau 382, Air France na 3 sau 380 sai Rynair na 4 da tashi sau 312. Kamfanin Pegasus ne ya zo na 5 da safara 297 sai KLM na 6 da safara 272.