Kamfanin Jiragen Saman Turkiyya (Turkish Airlines) ya bayyana cewa, daga ranar Juma'ar nan ya dawo da bayar da kayan makulashe a cikin jiragensa da ke safara tsakanin kasashen duniya.
A shekarar da ta gabata ne sakamakon annobar Corona kamfanin ya dakatar da bayar da abinci da abin sha a cikin jiragensa.
A yanzu ya dauki matakain dawo da hidimtawa matafiyan ne duba da yadda al'amura suke komawa daidai a kasashe da kuma yadda ake ta yi alluran riga-kafin Corona.
Darakta Janar na Turkish Airlines Bilal Eksi ya shaida cewa, daga ranar Juma'ar nan za a dawo da yin hidima a jiragensu da ke safarar kasa kasa.