Turkish Ailines ya tsawaita wa'adin dakatar da zuwa Isra'ila

Turkish Ailines ya tsawaita wa'adin dakatar da zuwa Isra'ila

Kamfanin jiragen saman Turkiyya ya kara wa'adin dakatar da tashi da sauka a Isra'ila har nan da 7 ga watan Fabrairu.

Sanarwar da aka fitar daga Ofishin Yada Labarai na Kamfanin ta ce, matakin da aka dauka a baya saboda killace masu Corona a Isra'ila da ya kare a ranar 31 ga Janairu, an kara shi zuwa 7 ga watan Fabrairu.

Jiragen kamfanin ba za su dinga zuwa Isra'ila ba.


News Source:   ()