Al'umar Turkawa na ciyar da Musulmai 700 a Najeriya abincin bude-baki a kowacce rana a wannan wata na Ramadhan mai albarka.
Wakilin Kungiyar Bayar da Taimakon Fatih Baloglu ya shaida cewa, Turkawa masu son yin karamci ne suka aiko da taimakon inda a rana ta 2 ta Ramadhan suka raba abinci ga Musulmai 700 da ke yankin Kuje na Babban Birnin Tarayya Abuja.
Baloglu ya ce, a kowacce rana ta Ramadhan za a ciyar da masu azumi 700 a yankunan Abuja daban-daban, kuma ta wannan aiki suna da niyyar ciyar da mutane dubu 20.
Baloglu ya ce, "Muna jin dadin yadda mu ke tara 'yan uwanmu Musulmai a nan. Akwai bukatar mu taimakawa junanmu a watan azumin Ramadhan.
Daya daga cikin wadanda suka halarci bude-bakin Abubakar Sharif ya ce, yana mika godiyarsa ga Turkawan da suka aika da kayan taimakon inda ya ce,
"Ba mu da abun da za mu yi Turkawa sakamakon wannan taimako sai dai Addu'a. Za mu yi ta yi wa Turkawa Addu'a.