Tunisiya na neman mafita daga matsin tattalin arziki

Tunisiya na neman mafita daga matsin tattalin arziki

A Tunisiya da ake neman mafita daga matsin tattalin arziki, Fadar Shugaban Kasar ta shirya amfani da matasa wajen shiga shirin amfani da kafafan sadawar na zamani.

Sanarwar da Fadar Shugaban Kasar Tunisiya ta fitar ta ce, Shugaba Kays Said ya karbi bakuncin tsohon Ministan Kudi Binzar Yaish a Fadar Kartaca.

A ganawar da suka yi, Said ya bayyana cewa, a shirye su ke su samar da wani shiri na sulhun kasa da daukacin matasan Tunisiya za su shiga ciki don fita daga rikicin tattalin arziki da ake ciki.

Ya ce, domin fita daga matsin tattalin arzikin da ake ciki, sun dauki kwararan matakai, kuma kowa zai amfana da wannan shiri na cigaban kasa bisa adalci, kuma wannan wani mataki ne da zai kyautata makomar kasar.

Tsohon Minista Yaish kuma ya baiyanawa Shugaban Kasar tsarin sadarwa na zamani da zai taimaka wajen samun nasarar shirin.

Yaish ya kuma bayar da bayanai game da yanayin tattalin arziki, kudaden jama'a, kasafin kudi da irin yadda matsalolin da suke ciki suke barazana ga kasar kai tsaye, ya kuma bayar da shawarwarin da za a yi aiki da su don fita daga matsalolin tattalin arzikin da Tunisya ta ke ciki a yau.

Fadar Shugaban Kasar Tunisiya ta amince da kiran da Tarayyar Kungiyoyin Kwadago suka yi na shirin Sulhun Kasa don Cigaba wanda aka fara a ranar Talatar nan.


News Source:   ()