TIKA ta gina sashen kula da yara a wani asibitin Pakistan

TIKA ta gina sashen kula da yara a wani asibitin Pakistan

Hukumar Hadin Kai da Cigaba ta Turkiyya (TIKA) ta gudanar bukin bude sashen kula da yara kanana da ke cikin mawuyacin hali a wani asibiti da ke garin Karachi na Pakistan.

Sanarwar da aka fitar daga TIKA ta bayyana cewa, wannan ne dakin kula da yara da ke cikin mawuyacin hali sakamakon cutar gurbatar jini na farko a Pakistan. Dakin na da gadaje 10.

A ranar 27 ga watan Janairu ma TIKA ta samar da dakin tiyata ga yara masu ciwon lebe da dasashi a wani asibitin na garin Karachi.

Haka zalika TIKA ta samar da na'urar daukar hoton marasa lafiya da a shekara ta ke hidimtawa mutane dubu 6 kyauta a garin na Karachi.

 


News Source:   ()