TIKA ta fara rabon kayan abinci da tsafta ga al'umar Kenya

TIKA ta fara rabon kayan abinci da tsafta ga al'umar Kenya

Hukumar Cigaba da Hadin Kai ta Turkiyya (TIKA) ta fara rabon kayan abinci da na tsafta ga iyalai 1,200 da ke Kenya.

Jami'in TIKA a Nairobi Eyup Yavuz Umutlu ya shaida cewa, a watan Ramadhan za su bayar da kayan abinci da na tsafta ga iyalai dubu 1,200. Kuma kayan abincin ya kai yawan tan 36.

Umutlu ya ce, "A unguwar South Kariobangi da ke Babban Birnin Nairobi an bayar da kunshin kayan abinci da na tsafta guda 215 ga mabukata da gidajen marayu."

Umutlu ya kuma ce, za su raba kayan abincin da na tsafta ga jama'ar Kenya a tsawon watan Ramadhan.

Ya ce, "A wannan shekarar mun bayar da fifiko na musamman ga gidajen marayu. Muna bayar da abinci da taimako ga ga mabukata ba tare da duba zuwa ga addini, yare ko launin fata ba, wanda dabi'a ce ta kakanninmu da muka gaba."


News Source:   ()