A cikin shekarar 2020 tattalin arzikin Koriya ta Kudu ya yi raguwar da bai taba irinsa ba a cikin shekaru 22 sabili da matsalolin da Korona ke haifarwa kamar yadda babban bankin kasar ta sanar.
Dangane ga wasu alkaluman da babban bankin kasar ya fitar kudaden shigar kasar sun ragu da kaso 1 cikin dari daga shekarar bara idan aka kwatanta da na 2019.
An bayyana cewa wannan ne dai raguwar karfin tattalin arziki a shekara mafi muni na farko tun daga shekarar 1998 lokacin da kasar ta fuskanci matsalolin tattalin arziki.
Kamar dai yadda Korona ke yiwa kasashe illa ita ma Koriya ta Kudu ba ta kasance ware ba, inda a halin yanzu mutum dubu 91,240 suka kamu da cutar yayinda dubu 1,619 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar.