An sanar da cewa tashin farashin gangan gurbataccen man fetur zai kasance lamarin da zai bunkasa tattalin arziki.
Farashin gangan man ya karu zuwa dala 68.28 lamarin dake nuna karin kaso 0.55 cikin dari daga dala 67.90.
A Amurka a kasuwar West Texas Intermediate (WTI) farashin ya karu zuwa dala $64.83 lamarin dake nuna karin kaso 0.60 cikin dari daga dala $64.44.
Tashin farashin man zai kasance abinda zai shafi farashin wasu kayayyakin da ake amfani dasu yau da kullum lamarin da zai iya haifar da bunkasar tattalin arziki.
News Source: ()