Hukumar Tarayyar Turai ta kiyasta cewa tattalin arzikin Turkiyya zai bunkasa da kaso 5.2 a 2021 da kuma 4.2 a 2022.
Hukumar ta Turai ta wallafa rahotonta "Hasashen Tattalin Arzikin Turai na Bazarar 2021".
A cikin rahoton, an tunatar da cewa tattalin arzikin Turkiyya ya bunkasa da kaso 1.8 a bara duk da sabon nau'in kwayar cutar coronavirus, kuma an kiyasta cewa zai karu da kashi 5.2 cikin dari a 2021 da kuma 4.2 a 2022.
A rahoton da ya gabata, wanda ya hada da kiyasi ga tattalin arzikin Turkiyya, an bayyana cewa tattalin arzikin Turkiyya ya ragu da kaso 2.5 cikin dari inda kuma aka yi hasashen cewa zai bunkasa da kaso 3.9 cikin dari a shekarar 2021.
A gefe guda kuma, an yi hasashen bunkasar tattalin arzikin yankin Turai na 2021 zuwa kashi 4.3. cikin dari.