Tarayyar Turai ta bayar da Euro miliyan 300 ga Tunisia, Euro miliyan 80 zuwa Arewacin Macedonia, Euro miliyan 50 ga Kosovo da Euro miliyan 30 ga Montenegro.
Hukumar ta EU ta ba da sanarwar cewa an ba da tallafi na kudi ga kasashe 4 domin rage radadin da Korona ke haifarwa.
A cikin sanarwar, an yi nuni da cewa kasashe 4 sun cika sharuddan iya samun tallafin kamar tsarin majalisa mai jam'iyu da yawa, mutunta 'yancin dan adam, bin doka da kuma ingantattun hanyoyin dimokiradiyya.
Kungiyar ta EU na iya ba da tallafi na kudi ga kasashen da ke kusa da ita a lokacin rikicin tattalin arziki.
Tarayyar Turai na bayar da tallafin kudi ne ga kasashen da suka cika sharudan da ta tsara.
News Source: ()