Tarayyar Turai da Turkiyya na tattaunawa akan daukar nauyin taron bunkasa kanana da matsakaitan kanfuna (SMEs) da za’a gudanar daga 15 zuwa 16 ga watan Maris a Ankara.
Hakan zai bada damar bunkasa kanfuna da basu damar fafatawa a kasuwancin yau da kullum domin cimma burin da ake bukata.
Ministan kimiyya da fasaha kasar Turkiyya Mustafa Varank da shugaban tawagar Turai Nikolaus Meyer-Landrut zasu halarci taron.
A taron za’a tattauna akan kimiyyar dijital da kuma irin kalubalen da annobar Korona ta haifar da kuma yadda za’a magancesu.
News Source: ()