Sudan: Gaza cimma matsaya kan Madatsar Ruwa ta Hedasi na da hatsari

Sudan: Gaza cimma matsaya kan Madatsar Ruwa ta Hedasi na da hatsari

Ministan Kula da Madatsun Ruwa na Sudan Yasir Abbas ya sanar da cewa, gaza cimma matsaya kan Madatsar Ruwa ta Hedasi da Itopiya ta gina a Kogin Nil na da hatsari ga kasashen yankin.

Sanarwar da Ma'aikatar Kula da Madatsun Ruwa ta Sudan ta fitar a lokacin da ta karbi bakuncin wani jami'in Tarayyar Turai ta bayyana cewa,

"Madatsar Ruwa ta Hedasi na da amfani ga Sudan amma idan aka kasa cimma matsayar hadaka da yarjejeniya bisa doka, to hakan zai cutar da kasashen yankin."

Abbas ya kara da cewa, Madatsar Ruwa ta Hedasi za ta illata Matsasar Ruwa ta Rusayris tare da yankunan da ake yin nona a Sudan.

 


News Source:   ()