SpaceX ya sake harba taurarin dan adam 60 zuwa sama

SpaceX ya sake harba taurarin dan adam 60 zuwa sama

Kamfanin Bincike a Sararin Samaniya na SpaceX mallakar Elon Musk ya sake harba taurarin dan adam 60 zuwa duniyar sama.

A karo na 22 kenan aka harba taurarin dan adam karkashin shirin Starlink inda ake amfani da kumbon Falcon 9.

An harba taurarin a cibiyar 'yan sama jannati ta Cape Canaveral da ke Florida.

SpaceX na harba taurarin dan adam zuwa sama a karkashin aikin Starlink na samar da yanar gizo.

Nan da shekarar 2027 SpaceX na da manufar harba taurarin dan adam dubu 12,000 zuwa sama.

 


News Source:   ()