Sinovac zai dinga samar da riga-kafin Corona biliyan 2 a kowacce shekara

Sinovac zai dinga samar da riga-kafin Corona biliyan 2 a kowacce shekara

Kamfanin Sinovac na kasar China ya bayyana cewa, a kowacce shekara zai dinga samar da allurar riga-kafin Corona guda biliyan 2.

Sinovac ya shaida cewa, an kammala gwaji na 3 na allurar da suka samar, kuma za a iya fara yi wa mutane.

Kamfanin ya ce, tuni ya fara samar da allurar da yawa kuma yana da karfin samar da kwaya biliyan 2 a kowacce shekara.

Bayan kamfanin ya bude reshe a Beijing Babban Birnin China, adadin alluran da zai samar ya ninka sau 2.

A watan Agustan 2020 kamfanin ya ce, za su iya samar da kwaya miliyan 500 a kowacce shekara. A watan Fabrairun bana kuma ya sanar da za su iya samar da biliyan 1.

 


News Source:   ()