Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai gana da jagororin manyan kamfanonin Amurka.
A ganawar da za a yi ta hanyar sadarwar bidiyo da shugabannin manyan kamfanoni 20 na Amurka, za a mayar da hankali kan batun zuba jari na hadin gwiwa a Turkiyya.
Shugaba Erdogan zai baiyanawa kamfanonin na Amurka irin tagomashin da kamfanonin kasashen waje suke samu idan suka zuba jari a Turkiyya, zai bayyana musu damarmakin zuba jari a kasarsa.
Shugaba Erdogan zai kuma amsa tambayoyin jagororin kamfanonin.
News Source: ()