Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fitar da sanarwa game da motar bas mai aiki da lantarki da Injiniyoyin Turkiyya suka samar.
Ya ce "In sha Allah wannan abu zai zamar mana abun tutiya, a lokacin da duniya ta ke bukatar makamashi mai tsafta."
Shugaba Erdogan ya fitar da sanarwar game da wannan cigaba ta shafinsa na Telegram.
Erdogan ya dauki hoto a gaban motar bas din tare da yadawa inda ya ce,
"'Yan uwana masoyana, a yau mun gwada tashin motar bas dinmu mai aiki da lantarki a kulliyya, motar na da sunan ATAK Elektric. Mota ce da kamfanunnukan KARSAN da ADASTEC, In sha Allah wannan abu zai zamar mana abun tutiya, a lokacin da duniya ta ke bukatar makamashi mai tsafta."