Sakamakon karar zirarar mai ta tsawon shekaru 31 da aka shigar, kamfanin haka da kasuwancin albarkatun man fetur na Shell ya amince da ya biya diyyar dala miliyan 110 ga jama'ar Ogoni na Najeriya.
Alkalin Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ya bayar da umarnin a biya diyyar a cikin kwanaki 21 masu zuwa.
Lauyan Shell ya bayyana cewa, kamfanin da yake wakilta ya amince da ya biya kudin.
Tsawon shekaru 31 al'umar Ogoni suka kai karar kamfanin Shell sakamakon kwarar mai a yankinsu da kamfanin ya janyo.
Tun shekarar 1958 kamfanin Shell ya fara hakar albarkatun mai a yankin Niger Delta na Najeriya inda a kowacce shekara mai yake zirara daga bututu da rijiyoyin da yake aiki da su.
A watan Janairu kamfanin mai na Shell ya amince da ya biya diyyar dala miliyan 84 tare da tsaftace Kogin Bogo sakamakon zirarar mai a shekarun 2008 da 2009.