An bayyana cewa, a cikin shekaru 3 da suka gabata yara kanana 'yan gudun hijira sama da dubu goma sha takwas ne suka bata a nahiyar Turai, kuma ana tunanin sun fada hannayen masu aikata muggan laifuka.
Jaridar De Standard ta Beljiyom da Kungiyar Zurfafa Binciken Aikin jarida ta Knack ne suka gudanar da wani bincike mai suna "Lost In Europe" (Bata a Turai), inda suka gano cewa, tun daga shekarar 2018 zuwa yau yara kanana dubu 18,292 da suka tafi Turai ba tare da iyayensu ba sun yi batan dabo.
Ana hasashen kungiyoyin bata-gari ne suka dibi yaran kuma suke amfani da su ta wata hanyar ko kuma an saka su aiyuka ta karfi da yaji.
An bayyana cewa, mafi yawan yaran kanana sun fito daga kasashen Morocco, Aljeriya, Eritiriya, Gini da Afganistan.
A binciken an bayyana cewa, sakamakon yadda a kasashe irin su Faransa da Romaniya ba a dauki bayanan yaran da suka bata ba, akwai yiwuwar adadin ya haura yadda aka gano a yanzu.
Haka zalika rahoton ya bayyana cewa, sakamakon annobar Corona da ta janyo raguwar gudun hijira, adadin yaran da suka bata a shekarar 2020 ya yi kasa da shekarun da suka gabace ta.
Aikin binciken ya kuma kara da cewa, yadda kasashen Turai ba su yi aiki da hanya iri daya ba wajen tattara bayanai game da yaran kanana da suka bata, ya sanya an shigar da bayanan ta hanya mara kyau.
Mambar Hukumar Tarayyar Turai Mai Kula da Harkokin Cikin Gida Ylva Johansson ta shaida cewa, sun damu matuka game da samun labarin batan yaran kanana, kuma sun dora alhakin hakan kan kasashen da yaran suka bace a cikin su.
Rundunar 'Yan sandan Turai ta bayyana cewa, a shekarar 2016 akalla yaran masu gudun hijira dubu 10,000 ne suka yi batan dabo a nahiyar.