Ruhani: Mafita daya ita ce Amurka ta cire mana dukkan takunkumai

Ruhani: Mafita daya ita ce Amurka ta cire mana dukkan takunkumai

Shugaban Kasar Iran Hassan Ruhani ya bayyana cewa, babu wani zabi da ya rage illa Amurka ta janye musu dukkan takunkuman da suka sabawa yarjejeniyar nukiliya.

Ruhani ya gana da Shugaban Alkalai Ibrahim Reis da Shugaban Majalisar Dokoki muhammad Bakir Kalibaf a Tehran Babban Birnin Iran inda ya bayyana cewa, Amurka ta amince kan ba ta yi nasara ba a manufofinta na adawa da Iran.

Ya ce, "Yadda Amurka ta furta ba ta yi nasara kan manufofinta na adawa da Iran ba, nasara ce ga kasarmu. A yau babu wani zabi da ya rage illa Amurka ta janye musu dukkan takunkuman da suka sabawa yarjejeniyar nukiliya."


News Source:   ()