Rasha ta kara yawan tumatur da take saya daga Turkiyya

Rasha ta kara yawan tumatur da take saya daga Turkiyya

Rasha ta bayyana shirin karin yawan  tumatir din da take saya daga Turkiyya lamarin da ya biyu bayan kiraye kirayen da masu fitar da tumatir din daga Turkiyya suka yi.

Kamar yadda bayanai suka bayyana, ma’aikatar harkokin gonar kasar Rasha ta sanar da cewa za ta kara yawan tumatir din da kasar ke saya daga Turkiyya da ton 50,000 inda yawan zai kai ton dubu 300,000.

Masu fitar da tumatir daga Turkiyya sun yi kiran ne a yayinda wa’adin yawan tumatir da suke fitarwa zuwa Rasha na ton dubu 250, 00 ke daf ga karewa.

Rasha ta kara yawan tumatir din da farko a watan  Febrairu da ton 50,000 daga dubu 200,000 zuwa dubu 250,000.


News Source:   ()