Mataimakin Shugaban Kasar Turkiyya Fuat Oktay ya bayyana cewa, a watanni 3 na farkon 2021 tattalin arzikin kasar ya habaka da kaso 7 cikin 100 wanda shi ne mafi habaka a tsakanin kasashen G20 masu karfin tattalin arziki a duniya.
A sanarwar da Oktay ya fitar ta shafin sada zumunta ya bayyana cewa,
"A watanni 3 na farkon 2021 tattalin arzikinmu ya habaka da kaso 7, shi ne na 2 a jerin kasashe mambobin G20. Mun fadi za mu yi juya yanayin annobar da aka fada don samun ci gaba. A kowacce rana Turkiyya na habaka na kara girmama.
News Source: ()