Nukiliya: Iran ta yi watsi da shawarar Tarayyar Turai

Nukiliya: Iran ta yi watsi da shawarar Tarayyar Turai

Iran ta yi watsi da shawarar da Wakilin Tarayyar Turai Kan Harkokin Kasashen Waje da Manufofin Tsaro Joseph Borrel ya bayar na a gudanar da taro kan makamin Nukiliya ba a hukumance ba, inda ta ce yanzu ba lokaci ne da ya dace a yi hakan ba.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Said Hatibzade ya yi bayani a wata rubutacciyar sanarwa da aka fitar a shafin yanar gizon Ma'aikatar.

Hatibzade ya ce, "Ba batu ne na bangarorin da suke a cikin yarjejeniyar su cika alkawarurrukan da suka yi ba. Shekaru 5 da suka gabata an yi irin wadannan zama na je-ka-na-yi-ka. Abun da ya kamata a yi a bayyane ya ke. Ya zama dole Amurka ta janye dukkan takunkuman da ta sakawa Iran tare da dawo da aiki da yarjejeniyar Nukiliya. Wannan abu ba ya bukatar taron kasa da kasa, ba ya bukatar hukuncin Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Kasa da Kasa."

Hatibzade ya kuma bayyana cewa, Amurka ba ta sauya halin ta ba, Shugaba Joe Biden bai rabu da matakan matsin lamba da tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya dauka ba, kuma bai bayyana za su aiki da yarjejeniyar Nukiliya ba.

Ya ce, "Iran za ta bayar da amsar harara da harara. Idan aka janye takunkumai, za ta sauya halinta ita ma. Idan aka dauki matakan nuna adawa, ita ma haka za ta mayar da martani. Iran za ta ci gaba da tattaunawa da Borrel da sauran masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar."


News Source:   ()