NASA da SpaceX sun dage lokacin dawowar 'yan sama jannati zuwa duniya

NASA da SpaceX sun dage lokacin dawowar 'yan sama jannati zuwa duniya

Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) ta dage lokacin dawowar 'yan sama jannati 4 da ke tashar bincike ta sararin samaniya su 4 zuwa  duniya wanda aka shirya a ranar Larabar nan.

Sanarwar da aka fitar daga NASA ta ce, 'yan sama jannati da suka hada da Amurkawa Michael Hopkins, Viktor Glover da Shannon Walker da dan kasar Japan Soichi Noguchi ba za su dawo duniya yanzu ba sabo rashin kyawun yanayi wanda ya hana kumbon Crew Dragon da zai dauko so tasowa.

An bayyana cewa, an dauki matakin bayan auna karfin iskar da ke tekun Florida inda aka shirya kumbon zai sauka.


News Source:   ()