A karkashin yaki da annobar Corona (Covid-19), Najeriya za ta sayi allurar riga-kafin cutar guda miliyan 29,8 daga wajen kamfanin Johnson&Johnson na Amurka.
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya ta Kasa ta Najeriya Faisal Shu'aib ya shaida cewa, kasar ta sanya hannu da Tarayyar Turai don sayen allurar riga-kafin J&J guda miliyan 29,8.
Shu'aib ya kara da cewa, nan da farko ko karshen watan Yuni Najeriya na sa ran karbar karin alluran riga-kafin Corona karkashin Shirin COVAX na kasa da kasa.
Ya ce, "Nan da wannan lokacin zai zama kasar ta kammala kashi na 2 na karbar allurar AstraZeneca."
A ranar 29 ga watan Maris Tarayyar Afirks ta sanya hannu da kamfanin Johnson&Johnson na Amurka don sayen allurar riga-kafin Corona guda miliyan 220.
A Najeriya ya zuwa yanzu an yi wa mutane sama da miliyan 1 allurar riga-kafin Corona da aka fara a ranar 5 ga Maris.