Gwamnatin Najeriya ta sanar da karbo fan stalin miliyan 4,2 da aka sace zuwa kasar Ingila daga jihar Delta a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar James Ibori.
Kakakin Ma'aikatar Shari'a ta Najeriya Dr. Umar Jibrilu Gwandu ya fitar da rubutacciyar sanarwa cewa, Ibori ya sace kudin gwamnati tare da mayar da su nasa, kuma an kwato fan stalin miliyan 4,2 daga hannun iyalansa da abokansa tare da dawo da su zuwa Najeriya.
Gwandu ya bayyana cewa, an saka kudin a asusun Naira na gwamnatin Najeriya.
A gefe guda, Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya ce, za a yi amfani da kudin don gina hanyoyi da gadoji a kasar.
A baya domin dawo da kudin, Malami ya sanya hannu da jakadiyar Ingila a Abuja Catriona Laing.
James Ibori ya shugabanci jihar Delta a tsakanin 1999-2007 kuma a shekarar 2012 kotun Ingila ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 sakamakon samun sa da laifin satar kudin gwamnati. A shekarar 2016 kuma aka sake shi.