An bayyana cewa, sama da mutane miliyan 100 na fuskantar matsanancin karancin abinci a nahiyar Afirka.
Tarayyar Kungiyoyin Red Cross da Red Crescent ta bayyana cewa, sakamakon rikicin da ake yi a nahiyar Afirka, sauyin yanayi, annobar farin dango, ambaliyar ruwa da matsin tattalin arziki ne ya sanya ake fuskantar karancin abinci.
Tarayyar ta ce, sama da mutane miliyan 100 na fuskantar karancin abinci a Afirka, kuma sakamakon annobar Corona matsalar ta kara ta'azzara a kasashe da dama.
Kasashen da suka fi fuskantar karancin abincin su ne: Sudan ta Kudu, Somaliya, Yankin Tigray na Itopiya, Yankin Tafkin Chadi, Burkina Faso, Mali da Nijar.