Mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wasu abubuwa a wata mahakar ma'adanai da ke tsakiyar China.
Tashar talabijin ta CGTN ta bayyana cewa, adadin leburori da suka mutu sakamakon fashewar da ta afku a mahakar ma'adanan kwal da ke jihar Hanan ya tashi zuwa mutum 4.
Mahukunta sun ce, ana ci gaba da neman wasu mutane 4 da suka bata.
A ranar 5 ga Yuni ne wasu abubuwa suka fashe a mahakar ma'adanan kwal da kamfanin makamashin lantarki na Hebi yake aiki a ciki.
News Source: ()