Ya zuwa yanzu mutane 17 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da mamakon ruwan sama ya janyo a Sri Linka.
Sanarwar da aka fitar daga Cibiyar Yaki da Ibti'la'o'i ta Sri Lanka ta bayyana cewa, tun ranar 3 ga watan Yuni ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar, kuma lamarin ya janyo ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa.
An bayyana sake gano jikkunan mutane 3 wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mutane 17.
Sanarwar ta ce a kalla mutane dubu 270 ne ambaliyar ta illata a yankunan Gampaha, Ratnapura, Kolombo, Puttalam, Kalutara, Kegalle da Galle, gidaje da dama kuma sun rasa hasken lantarki.
Hukumar Kula da Yanayi ta kasar ta sanar da cewa, ana sa ran raguwar ruwan saman amma a wasu yankunan za a ci gaba da yi.