Motoci masu aiki da lantarki sun fara yawo a Turkiyya

Wani kamfanin samar da ababan hawa da ke yankin Izmir na Turkiyya ya fitar da kananan motocin hawa masu aiki da lantarki wanda suka fara yawo a kan tituna.

A 'yan shekarun nan a Turkiyya ma ana ganin habaka a bangaren kimiyyar kere-kere kamar yadda ya ke a kasashen duniya da dama. Samar da motoci a Turkiyya na jerin aiyukan cigaban da ake yi.

Kamfanin KODECO da ke Izmir ya samar da kananan motocin hawa a cikin gari, kuma ya samu nasarar gwada motocin da ya samar.

Kamfanin ya samar da wata manhaja mai suna Zoop don amfani da motocin wanda hakan ya ke taimakawa a bangaren sufuri.

Motocin na iya tafiyar kilomita 100 idan aka cika su da caji.

Ana tayar da motar da bude kofofinta da manhajar Zoop. haka kuma ana saka giyar gaba da baya ta hanyar danna wani allo mai hoto na gilashi da ke cikin motar.

 


News Source:   ()