Motoci marasa matuka za su fara yawo a Jamus

Motoci marasa matuka za su fara yawo a Jamus

Gwamnatin Jamus ta samar da wani kudirin doka don kula da motoci marasa matuka da za su fara yawo a biranen kasar.

Sanarwar da aka fitar daga Ma'aikatar Sufuri ta Jamus ta ce, bayan majalisar zartarwa ta amince da kudirin dokar, an mika kudirin ga majalisar dokoki.

Sanarwar ta kara da cewa dokar ta tanadi "Mota mai tuka kanta a mataki na 4" za ta fara yawo, kuma hakan zai baiwa Jamus damar zama kasa ta farko a duniya da ta bayar da dama ga motocin su fara zirga-zirga.

 


News Source:   ()