A yunkurin hana sabon nau'in cutar Corona yaduwa a kasarta, gwamnatin Morocco ta sanar da dakatar da safarar jiragen sama tsakaninta da kasashen waje 5.
Sanarwar da aka fitar ta shafin Facebook na Hukumar Kula da Filayen Tashi da Saukar Jiragen Sama ta Morocco ta ce, an dauki matakin ne don hana yaduwar sabon nau'in cutar Corona (Covid-19).
A karkashin wannan mataki, an dakatar da safarar jiragen sama tsakanin Morocco da Mali, Gana, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Gini da Libiya har nan da watan Afrilu.
Sanarwar da Hukumar ta fitar a ranar 9 ga Maris ta ce, an dauki irin wannan mataki da kasashen Aljeriya, Masar, Girka, Finlan, Labanan, Norway, Polan da Kuwait.
A ranar 28 ga Janairu aka fara gangamin allurar riga-kafin Corona a Morocco, kuma alkaluman Ma'aikatar lafiya sun bayyana ya zuwa yanzu an yi wa mutane sama da miliyan 4,2 allurar.